<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>606</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 Ƴanuwa, ku zo mu bi Yesu
 Ƴanuwa, ku zo mu bi Yesu
 Yesu ne ya zama cetonmu.

[V2]
 Ƴanuwa ku bar ɗinkin laya
 Laya ba ya iya cece mu
 Yesu ne ya zama cetonmu
 Yesu ne ya zama cetonmu.

[V3]
 Ƴanuwa ku bar ɗinkin guru
 Guru ba ya iya cece mu.
 Yesu ne ya zama cetonmu
 Yesu ne ya zama cetonmu.

[V4]
 Ƴanuwa ku bar tsaka tsaka
 Ƴanuwa ku bar tsaka tsaka
 Ran da mutuwa ta zo, ta ɗauke ka.

[V5]
 A kira masu bi su zo su bizne ka
 Su zo su ƙi, su ce ba ka addininsa.
 Sa'annan kana tsaka tsaka.

[V6]
 A bizne ka babu yin addu'a,
 Ga Littafi Mai Tsarki ya shaida mu a nan
 Abin da aka ɗamre anan a duniya
 A ɗamre shi ya zama can samaniya
 Ƴanuwa ku bar tsaka tsaka
 Yesu ne ya zama cetonmu.</lyrics>
<title>Ƴanuwa, Ku Zo Mu Bi Yesu LW606</title>
</song>